A ranar Litinin shugaban hukumar fasa kwabri ta kasa kwastam, ya yi murabus daga mukaminsa.
A wata ganawa da ya yi da shugaba Muhammadu Buhari, Alhaji Dikko Inde ya mika wa shugaban kasar takardarsa ta murabus.
Babu bayani I zuwa yanzu game da dalilin murabus din nasa.
A watan Agustan shekarar 2009 ne Alhaji Inde mai shekaru 55 ya dare kujerar shugabancin hukumar ta kwastam.

No comments:
Post a Comment